Soyayya da hasuma na Janar

Jiu Baolian ya iya maganin cututuka 100 . Shi ne abu mai daraja na Zhou Hongde , likitan Sarki da ya riga ya ritaya . Wata rana an yi ambaliya mai tsanani Mr. Zhou ya ceci Liao Zhongping wanda yake fama da ciwo , kuma ya sa shi ya zama ‘dansa . A daidai wannan lokaci , matar tsohon sarki ba ta da lafiya . Saboda magani ba shi da mafani , Mr. Zhou ya mai da ‘dansa Zhaonian da ‘dansa ba na gaskiya ba Zhongping su tafi hedkwatar kasar don ba wa matar tsohon sarki magani mai kyau . Amma duk da haka a kan hanyar Zhongping ya manta da alherin da babansa ya kawo masa kuma ya tura Zhaonian, ‘dan Mr. Zhou na gaskiya daga tudu , kuma ya kwace magani mai kyau . Sa'an nan kuma ya zuwa hedkwatar kuma ya warke da matar tsohon sarki . Ba da dadewa ba Sarki ya nada shi ya zama jami'I mai kula da iyalai dubu 10 . Lokacin da ya koma gida , ya yi kariya cewa , Zhaonian ya fadi cikin ruwa kuma ya mutu . Don rufe bakin ‘yan iyalin Mr. Zhao , ya kone gidan iyalin Zhou , kuma ya tilasta Wanqing , diyar Zhou ta zama matarsa . Amma Wanqing ta tsalle cikin kogi ta mutu don kiyaye kirkinta .

Manya da kanana , ‘yan iyalin Zhou sun kubuta daga gobara . Zhou Hongde kuma yana damuwa cikin dogon lokaci har ya sami ciwo mai tsanani kuma ya ci basusuka masu yawa . Matar ‘dansa Shuxian ba ta da dabara sai ta sake auri Xiong Yemeng , Janar wanda ya jibge a iyakar kasar . Da suka yi aure ba da dadewa ba , makiya sun kawo hari a iyakar kasa . Sarki ya ba Yemeng umurni zuwa iyakar kasar don yaki da makiyan . Yemeng ya mika ‘dansa Xiong Heen wa matarsa Shuxian don raya shi .

A bayan shekaru 8 , Shuxian ta raya ‘danta Zhou Xiaoping da ‘dan mijinta Xiong Heen har su girma . A cikin jarrabawar duk kasar , su biyu sun ci nasara kuma sun zama jami'ai . A daidai wannan lokaci , Wanqing wadda aka cece ta daga ruwa ta kai kara a hedkwatar . Ba zato ba tsamani Zhou Xiaoping ya gana da innarsa Wanqing . A karshe dai su hada kansu sun kashe Zhongping kuma ‘yan iyalin Zhou sun yi murna da sake haduwa . ( Ado )اطلاعات:
داخلی بین المللی اخبار ایران، افغانستان و تاجیکستان اقتصادی فناوری ورزشی
فرهنگی
اطلاعات فرهنگی مسلمانان علمی و بهداشتی سرگرمی ویدیو موسیقی فرهنگ چین
گردشگری
گزارش ویژه جهان امروز اطلاعات خدماتی دیگر سیمای چین
امبادلات چین و ایران
مبادلات چین و ایران رویداد مهم در تاریخ چین و ایران گزارش تصویری کارشناسان و دانشمندان نمایشگاه دستاوردها
ویدیو
ویدیو
عکس ها
تصاویر گلچین
دانشنامه چین                آموزش زبان چینی